Majalisar wakilai ta dauki wani mataki da wasu ke gani abin alheri ne bayan jin irin koken da suka rika tashi kan batun korar ma’aikata 1,000 da Babban Bankin Najeriya CBN ya ce zai yi,
Yayin da kwararru a fanin tattalin arziki ke gani akwai bukatar kyakkyawan karatun ta natsu kan lamarin.
Majalisar ta ba Babban Bankin umurnin dakatarda sallaman ma’aikatan bankin ne domin ta Kafa Kwamiti na Musamman da zai yi bincike kan yadda za a yi wa ma’aikata 1,000 ritaya,
A lokaci daya kuma har za a biya su kudin sallama da ya kai Naira Biliyan 50 a wannan lokaci da kasa ke fama da rashin kudi, ta ce kwamiti ya yi bincike kan kai’doji da tsari da halarcin aikin.
A hirar shi da Muryar Amurka, dan Majalisa mai wakiltar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe Inuwa Garba ya yi karin haske cewa, Majalisa ita ce mai sa ido a yadda ake gudanar da mulki a kasa, saboda haka tana da hurumin daukar matakai kamar yadda doka ta tanada.
Inuwa ya ce babu yadda za a yi Majalisa ta bari irin wadannan matakai suna faruwa ba tare da ta duba yiwuwar haka a bisa tsari ba, dalilin da ya sa Majalisar ta kafa Kwamiti kenan.














































