Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya yi barazanar sallamar duk wani ma’aikacin da ya shiga yajin aiki nan da awa 72 idan bai koma aiki ba.
Gwamna Nwifuru, ya bayyana haka a ofishinsa da ke Abakaliki a lokacin da yake jawabi a game da yajin aikin da shugaban ƙungiyar ƙwadago na jihar, Kwamrade Comrade Oguguo Egwu ya fitar.
Oguguo, ya bayyana cewa yajin aikin biyayya ce ga umarnin shugaban ƙungiyar na ƙasa na ranar 8 ga Nuwamban 2024, inda ta yi kira ga ma’aikata a duk jihar da ba a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba su shiga yajin aiki.
Nwifuru, ya ce majalisar tarayya ba ta ƙayyyade sabon albashi ba, inda a cewarsa dokar ta yi magana ne kan mafi ƙarancin albashi
Ya ce ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi tun a watan Oktoba, shi ya sa ya yi mamaki da ya ga sun fara yajin aiki saboda haka babu wani ma’aikaci da yake bin bashin albashi ko fansho.
Gwamnan ya ƙara da cewa ya bayar da umarnin a fara ɗaukar sunayen waɗanda suke zuwa aiki, sannan ya ce babu maganar zaman sulhu, “saboda kwamrade Egwu ba ma’aikacinmu ba ne.














































