Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya kamata Nijeriya
da makwaftanta da ke yankin tafkin Chadi su ƙara ƙaimi
wajen sauya dokoki da ayyukan sojojin ƙasashen su.
Bola Tinubu ya ce, sauya dokokin aikin sojin ya zama wajibi, sakamakon yadda ƙasashen yankin ke fama da ƙaruwar tashe- tashen hankula.
Yayin da ya ke jawabi a wajen bikin yayen manyan sojoji kwas na 45 da aka gudanar a kwalejin sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna, shugaban Tinubu ya lissafo wasu kalubalen tsaro da ke fuskantar sojojin Nijeriya da na sauran ƙasashen yankin tafkin Chadi, waɗanda ya ce su na amfani da tsofaffin dokokin aikin soji.
Shugaba Tinubu ya ƙarfafa wa ƙasashen Afirka gwiwa wajen yin aiki tare domin kawar da kalubale guda da su ke fuskanta, sannan ya yaba da irin yunkurin da ƙasashen yankin tafkin Chadi ke yi na wanzar da zaman lafiya a yankin.
Ya ce hadin kan da ƙasashen yankin tafkin Chadin ke yi wajen yakar ayyukan ‘yan bindiga abin a yaba ne, amma ya yi kira da a sauya dokokin domin kawar da barazanar da su ke fuskanta