Home Labaru ‘Yan Najeriya Sai Sun Zuba Ruwa A Kasa Sun Sha Idan Kotu...

‘Yan Najeriya Sai Sun Zuba Ruwa A Kasa Sun Sha Idan Kotu Ta Soke Zaben Tinubu – PDP

45
0

Jam’iyyar PDP ta ce da zarar kotun sauraren ƙararrakin zaben
Shugaban Kasa ta soke nasarar Bola Tinubu ‘yan Nijeriya za
su zuba ruwa kasa su sha don murna.

Daraktan Tsare-tsare na Kwamitin Yakin Neman Zaɓen Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP Pedro Obaseki ya bayyana hakan a Abuja, inda ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa PDP ta na da yaƙinin kotun za ta yi shari’a mai adalcin da dukkan jam’iyyu za su aminta da ita.

Ya ce duba da irin gamsassun hujjojin da su ke da su, alƙalan kotun za su yi abin da ya dace.

Da ya ke tsokaci a kan karar da jam’iyyar APM da ke neman a soke zaben Tinubu ta shigar, Obaseki ya ce dole a duba batun cancanta.

Jam’iyyar APM dai ta kafa hujja da cewa Kashim Shettima ya haɗa takara biyu, wato ta Sanata da ta Mataimakin Shugaban Kasa kafin ranar zabe.

Leave a Reply