Home Labaru Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar

Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar

209
0
Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar
Zaben Kogi: PDP Ta Nada Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar

Jam’iyyar PDP ta nada kwamitin yaki neman zaben gwamnan jihar Kogi wanda zai gudana a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Da ya ke magana lokacin taron nada kwamitin, shugaban jam’iyyar na jihar Mr Samuel Uhuotu ya roki ‘yan kwamitin su yi yakin neman zabe mai cike da manufa.

Haka kuma ya shawarce su su guji furta kalaman batanci ga ‘yan jam’iyyun adawa a yayin gudanar da yakin neman zaben su.

Darakta kwamitin yakin neman zaben Tajudeen Yusuf ya ce kwamitin ya riga da ya kammala shirye-shiryen soma yakin neman kuri’u a lungu da sakon jihar, sanna ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa  INEC  ta shiri na musamman domin samu yin zabe cikin lumana da zaman lafiya.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya yi kira ga masu kada kuri’a su yi amfani da kuri’ar su ta hanyar da ta dace, domin tsamo kansu daga cikin halin kangin talauci.

A nasa jawabin dan takarar gwamnan karkashin jam’iyyar PDP, Musa Wada ya yi kira ga jama’a su fito kwansu da kwarkwatar su domin zaben jam’iyyar PDP ranar 16 ga watan Nuwamba.