Home Labaru Kiwon Lafiya Kula Da Lafiya: Zan Maida Hankali Wajen Inganta Fannin Kiwon Lafiya A...

Kula Da Lafiya: Zan Maida Hankali Wajen Inganta Fannin Kiwon Lafiya A Nijeriya – Osagie

435
0
Osagie Ehanire, Ministan Lafiya
Osagie Ehanire, Ministan Lafiya

Ministan lafiya Osagie Ehanire, ya ce zai maida hankali wajen ganin gwamnati ta fara aiki da dokar kiwon lafiya ta shekarar 2014 da aka gyara a Nijeriya.

Ehanire ya bayyana haka ne, yayin da ya ke tattaunawa da kwamitocin kiwon lafiya na majalisar dokoki ta kasa a wani taron da aka shirya a Abuja.

Ya ce tun a shekara ta 1999 zuwa yanzu, fannin kiwon lafiya a Nijeriya bai iya tabuka wani abin a zo a gani na inganta kiwon lafiyar ‘yan Nijeriya ba.

Ehanire, ya ce hakan ya na da nasaba ne da rashin amfani da dokokin inganta fannin, da rashin yin amfani da kudirori da shiriye-shiryen da za su taimaka wajen samar da ci-gaba a fannin.