Home Labaru Kasuwanci Tattalin Arziki: Za A Raba Wa Jihohi Kason Karshe Na Kudaden Paris...

Tattalin Arziki: Za A Raba Wa Jihohi Kason Karshe Na Kudaden Paris Club

385
0
Zainab Ahmed, Ministar Kudi
Zainab Ahmed, Ministar Kudi

Gwamnatin Tarayya, ta ce kwanan nan za ta raba wa jihohi cikon kudin Paris Club naira biliyan 649 da miliyan 434 da su ka yi saura.

Ministar kudi Zainab Ahmed ta bayyana haka, yayin da ta ke bayani a wajen taron manema labarai da ta shirya a Abuja.

Zainab ta ce, nan ba da dadewa ba za a fara raba wa jihohi kudaden, a matsayin kashin karshe na kudaden Paris Club da aka sha ba su a baya.

Ta ce tsarin ba jihohi kudaden Paris Club, ya samu gagarumar nasarar kai Nijeriya fita daga matsin tattalin arziki da ta yi fama da shi. Ministar ta kara da cewa, sakamakon nasarar shirin, yanzu haka Nijeriya ta hau hanyar dorewa a kan ingantaccen tattalin arziki.