Home Labaru Furuci: Hukumar DSS Ta Kama Manyan Malaman Musulunci Biyu A Katsina Da...

Furuci: Hukumar DSS Ta Kama Manyan Malaman Musulunci Biyu A Katsina Da Bauchi

894
0

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta kama wasu manyan Malaman addinin Musulunci a jahohin Katsina da Bauchi, wadanda su ka hada da Sheikh Aminu Usman da aka fi sani da Abu Ammar, da kuma Ustaz Idris Abdulaziz biyo bayan wata gayyata da hukumar tayi musu.

Wata majiya ta ce kimanin kwanaki biyar da suka gabata ne, hukumar DSS ta gayyaci Ustza Idris zuwa ofishinta dake Bauchi domin amsa tambayoyi, sai dai daga nan suka yi awon gaba dashi zuwa Abuja don ci-gaba da yi mashi tambayoyi.

Wani daga cikin almajiran Malamin, ya ce tun ranar Asabar data gabata basu samu damar tattaunawa dashi ba balle su san halin da malamin yake ciki.

Malam Abu Ammar kuma ya shiga hannu ne, bayan hukumar DSS ta gayyaceshi zuwa ofishinta a ranar Talatar da ta gabata, bayan wani wa’azi da yayi yana sukar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari game da tabarbarewar tsaro a Nijeriya.

Abu Ammar yana tare da wani abokinsa a lokacin da jami’an DSS suka kirashi a waya, suna gayyatarsa zuwa ofishinsu dake kan hanyar Daura a garin Katsina.Idandaizaa tunawa, hukumar DSS ta taba kama Malam Abu Ammar a watan Maris na shekara ta 2015, biyo bayan wasu kalamai daya furta akan tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema.

Leave a Reply