Home Labaru Takadama: Kotu Ta Yanke Hukunci A Kan Sauya Shekar Saraki Da Dogara

Takadama: Kotu Ta Yanke Hukunci A Kan Sauya Shekar Saraki Da Dogara

437
0

Wata babbar kotu da ke zama a Abuja, da zartar da hukuncin cewa sauya shekar da ‘yan majalisun tarayya 53 su ka yi zuwa wasu jam’iyyu siyasa ya saba wa doka kamar yadda rahotanni su ka ruwaito.

A yayin zartar da hukuncin, Mai shari’a Okon Abang, ya ce ‘yan majalisar ba su gabatar da gamsassun dalilan da zai ba su damar ficewa daga jam’iyyun su ba.

Hukuncin da ya biyo bayan wata kara ne da kungiyar kare martabar shari’a LEDAP, ta shigar, ta na kallubalantar sauya shekar da Bukola Saraki da Yakubu Dogara Yakubu Dogara da wasu ‘yan majalisa 51 su ka yi.

LEDAP ta bukaci kotu ta umurci ‘yan majalisar su yi murabus daga kujerun su sakamakon sauya shekar da su ka yi, su kuma maida albashi da allawus-alawus da su ka karba tun bayan ficewa daga jam’iyyun da su ka ci zabe a karkashin su. Kungiyar ta yi ikirarin cewa, ‘yan majalisar sun fice daga jam’iyyunsu ne saboda son rai, ba domin rabuwar kawunna a jam’iyyun su kamar yadda doka ta tanada ba.