
Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirinta na kashe Naira tiriliyan 12 da biliyan 66 a matsayin kasafin shekara ta 2021, yayin da kasafin da ake shiryawa zai zo da gibin Naira tiriliyan 5 da biliyan 16.
Rahotonni sun bayyana cewa, dole gwamnatin tarayya za ta nemo bashin Naira tiriliyan 4 da miliyan 28.
Gwamnatin wadda ta dogara da arzikin man fetur za ta fito da ragowar gibin da za a samu ne daga harajin da za a tatsa a cikin gida.
A ranar Talatar da ta gabata ne, shugaba Buhari ya gabatar da tsarin tattalin arziki a gaban majalisar tarayya domin su amince da tsare-tsaren sa, na kashe kudi.
A kasafin shekara mai zuwa, gwamnatin za ta na hangen Naira tiriliyan 5 da biliyan 75 a matsayin kudin da za a batar a kan albashi da tafiyar da harkokin gwamnati.
Naira tiriliyan 3 da biliyan 12 kuma za su tafi a biyan bashin da ake bin Nijeriya, yayin da za a nemi karbo wani sabon bashin Naira tiriliyan 4 da biliyan 200, sannan a shekara ta 2021, 1 bisa 3 na kasafin da aka tsara zai fito ne daga bashin da za a ciwo.
You must log in to post a comment.