Home Labaru Kiwon Lafiya Cutar Korona: A Kowacce Rana Majinyaci Ya Na Cin N1m – Kwamishina

Cutar Korona: A Kowacce Rana Majinyaci Ya Na Cin N1m – Kwamishina

348
0

Kwamishinan lafiya na jihar Legas Akin Abayomi, ya ce gwamnati na kashe tsakanin Naira dubu 500 zuwa miliyan daya a kan kowanne mai cutar korona a jihar idan ta tsananta.

Yayin zantawa da manema labarai, Abayomi ya ce yawan kudin da ake kashewa majinyatan korona ya danganta ne da tsananin da cutar ta yi.

Kwamishinan, ya ce su na kashe kusan Naira dubu 100 a kan majinyacin cutar da ba ta yi wa tsananin kamu ba, domin maganin cutar ga wanda ba ta tsananta ba ko ta ke tsaka-tsaki a cibiyar killacewa su na kashe Naira dubu 100 ne a rana daya.

Ya ce wannan kawai zai iya bada damar kintatar yawan kudin da gwamnati ke kashewa a kan cibiyar killacewa da kuma magani tare da jinya. 

Kwamishinan ya kara da cewa, idan mutum ya na bukatar kulawa sosai ko halin da majinyaci ya ke ciki ya tsananta, su na iya kashe Naira dubu 500 har zuwa miliyan daya a rana daya.