Home Labaru Tattalin Arziki: Buhari Ya Ƙaddamar Da Aikin Titin Jirgin Ƙasa Daga Kano...

Tattalin Arziki: Buhari Ya Ƙaddamar Da Aikin Titin Jirgin Ƙasa Daga Kano Zuwa Maraɗi

219
0

Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya ƙaddamar da titin jirgin
ƙasa da zai tashi daga Kano ya ratsa Katsina da Jibiya zuwa
Maraɗi a jamhuriyar Nijar.

A bikin ƙaddamar da aikin, wanda shugaba Buhari ya halarta ta
yanar gizo, ya ce titin zai bi ta manyan cibiyoyin kasuwanci da
su ka hada da Kazaure da Daura da Katsina da kuma Maraɗi.

Shugaba Buhari, ya ce aikin zai tabbatar da ci-gaban kasuwanci
tsakanin Nijeriya da Nijar, kuma zai inganta hanyoyin samun
kuɗin shiga ga ƙasashen biyu.

Kamfanin Messrs Mota-Engil Nigeria Limited ne ke aikin
shimfida titin, kuma zai gina wata makarantar koyon kimiyyar
sufuri da titin jirgin ƙasa.

Shugaba Buhari, ya yi kira ga masu zuba jari su sa hannu don
ganin an samu ci-gaba a fannin tattalin arziƙi.