Home Labaru Agaji: Gwamnati Ta Kashe N37bn A Tallafin ‘Survival Fund’ — Osinbajo

Agaji: Gwamnati Ta Kashe N37bn A Tallafin ‘Survival Fund’ — Osinbajo

207
0
Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce
gwamnatin Tarayya ta kashe Naira biliyan 37 a kan shirin tallafa
wa ‘yan Nijeriya na Survival Fund a Turance.

Ya ce an kashe kudin ne a kan wasu tsare-tsare, wadanda su ka
hada da Naira dubu 50 ga masu aiki a ma’aikatu na tsawon
watanni uku zuwa sama da aka raba wa mutane dubu 300.

An kuma tallafa ma wasu masu sana’ar hannu kusan dubu 100
da Naira dubu 30, da rajistar sunan kasuwanci a hukumar yi wa
kamfanoni da masana’antu rajista na mutane dubu 100, wadada
duk gwamnatin Tarayya ta biya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban
kasa Laolu Akande ya fitar, ya ce shirin Survival Fund wani
bangare ne a karkashin shirin dorewar tattalin arziki na
gwamnatin shugaba Buhari.

Sanarwar ta cigaba da cewa, ministoci da shugabannin
hukumomin sun kasance su na bada rahoton ci-gaban da aka
samu na aiwatar da shirin.