Home Labaru Ibrahim Abdulaziz Na Muryar Amurka Da Liberty Tashar ‘Yanci Ya Rasu

Ibrahim Abdulaziz Na Muryar Amurka Da Liberty Tashar ‘Yanci Ya Rasu

350
0

Allah Ya Yi wa tsohon dan jarida Ibrahim Abdulazeez rasuwa.

Ibrahim Abdulaziz kafin rasuwarsa wakilin gidan Radiyon Muryar Amurka (VOA) Da Liberty Radio da TV ne a Yola, Jihar Adamawa.

Ya rasu ne sakamakon hatsarin mota tsakanin Alkaleri da Bauchi, ya rasu ya bar mata da yara.

A lokacin rayuwarsa, Ibrahim Abdulazeez, ya yi aiki da gidan Rediyon Liberty, a matsayin babban wakilinta a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ya kuma yi aiki da gidajen rediyon Gotel da Fombina FM Yola, mallakin Gwamnatin Tarayya, kuma shi ne kuma mawallafin jaridar Adamawa Times.

Kafin nan, ya kuma yi aiki da gidan rediyon Nagarta da ke Kaduna.