Home Labaru Sabanin Hankali: Kotu Ta Daure Wanda Ya Zargi Gwamnan CBN Da Satar...

Sabanin Hankali: Kotu Ta Daure Wanda Ya Zargi Gwamnan CBN Da Satar Biliyoyin Naira

275
0

Wani mutum da ya fallasa zargin gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele da tafka almundahana, ya samu matsugunni a gidan yari bayan ya ce Emefiele bai cancanci ya zarce a matsayin gwamnan CBN na wani zango ba.

Kotun dai ta bada umarnin a tsare George Uboh a gidan yarin Suleja, bayan Emefiele ya shigar da karar zargin sa da yunkurin bata ma shi suna.

Lauyan Emefiele John Mary Jideobi, ya ce an kama Uboh ne a harabar kotu bayan an bada belin sa a kan wata shari’a ta daban.

Rahotanni sun ce, Uboh ne ya fara shigar da karar Emefiele a gaban wata kotun tarayya da ke Abuja, inda ya kalubalanci yunkurin gwamnatin tarayya na sake nada Emefiele a matsayin gwamnan CBN karo na biyu.

Uboh ya kuma zargi Emefiele da hada kai da kamfanin NNPC su ka zambaci ‘yan Nijeriya kudaden da yawan su ya kai naira biliyan 500.

Duk da kotu ta nemi Emefiele ya bayyana domin kare kansa, bai yi hakan ba har majalisa ta tabbatar da shi. Jami’an ‘yan sanda na rundunar binciken miyagun laifuka (FCID) ne suka kama Uboh kafin daga bisani su gurfanar da shi a gaban kotu.

Leave a Reply