Home Labaru Nasara: An Saki Muntari Yusuf Wanda Aka Yi Garkuwa Da Shi A...

Nasara: An Saki Muntari Yusuf Wanda Aka Yi Garkuwa Da Shi A Kaduna

449
0

Masu garkuwa da mutane sun saki mai magana da da yawun hukumar kula da yanayi ta kasa Muntari Yusuf, wanda aka yi garkuwa da shi a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Wadanda suka yi garkuwa da shi sun sake shi ne a yammacin ranar Juma’a wanda ya yi daidai da yammacin auren ‘yar’sa.
Iyalansa da ‘yan uwa da abokan arziki ne suka tattara kudin naira miliyan 50 ga masu garkuwa da mutanen, kwanaki hudu bayan sun yi garkuwa da shi.
Rahotanni sun ce yadda aka sace Yusuf, shi ne masu garkuwan sun zo da moto guda biyu inda ta farkon ta toshe gaban motar sa kirar Peugeot 408, a ya yin da dayan kuma ta tare shi ta baya.
Rahotannin sun ce Muntari Yusuf, ya umurci iyalansa su siyar da motarsa, sannan su cire naira miliyan biyu da suka rage a asusun bankinsa domin biyan kudin fansar sa.

Leave a Reply