Ana zargin wasu ‘yan kasar China biyu da yin kutse a ayyukan daruruwan kamfanoni a fadin duniya, ciki har da kamfanin nazarin halitta da suke kokarin fitowa da maganin rigakafin COVID-19 da kuma jinya.
Ana zargin Li zaoyu mai shekaru 34 da Dong Jiazi mai shekaru 33 da aikata laifuka 11 a gundumar gabashin jihar Washington a ranar Talata.
Wannan da shine karon farko da masu shigar da kara a Amurka suka zargi masu kutsen China da aikata laifi da suka bayyana da babbar barazana na yin aiki da kasar China.
Shugaban sashen tsaron kasa a ma’aikatar shari’a ta Amurka John Demers, ya zargi China da taimakawa masu aikata laifin kutse.














































