Home Labaru Taron Ecowas: Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Burkina Faso Ranar Asabar

Taron Ecowas: Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Burkina Faso Ranar Asabar

402
0
Kasafin Kudi: Buhari Ya Dakatar Da Ministoci Daga Zuwa Kashashen Ketare
Kasafin Kudi: Buhari Ya Dakatar Da Ministoci Daga Zuwa Kashashen Ketare

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai tafi birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso a ranar Asabar, domin halartar taron kungiyar bunkasa tattalin arkin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS, da kuma taron musamman a kan yaki da ta’addanci.

Karatan Wannan: Taron Kasar Japan: Shugaba Buhari Ya Dawo Gida Najeriya

Shugabanin kasashen Afrika ta Yamma dai sun kira taron ne, domin bita a kan matakan da su ka dauka a kan yaki da ta’addanci, a wani mataki na sanin matakan da za su dauka domin inganta yaki da ta’addanci saboda matsalar ta na karuwa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina, ya ce shugabanin kasashen sun yanke shawarar yin taron ne, yayin wani taro karo na 55 da aka yi a ranar 29 ga watan Yuni a Abuja.

Sanarwar ta ce, Shugaba Buhari ya yi na’am da hadin kai wajen yaki da ta’addanci, kuma zai cigaba da hadin gwiwa da kasashen ECOWAS da sauran kungiyoyin kasa da kasa domin magance matsalar.

A wajen taron da za a gudanar, ana sa ran shugabannin ECOWAS za su cimma matsaya a kan shirin yaki da ta’addanci, tare da sa ido a kan yadda za a kaddamar da shirin don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.