Home Labaru Matsalar Tsaro: Babagana Monguno Ya Ce Ana Shigo Da Muggan Makamai Nijeriya

Matsalar Tsaro: Babagana Monguno Ya Ce Ana Shigo Da Muggan Makamai Nijeriya

625
0
Muggan Makamai
Muggan Makamai

Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Mungono, ya ce ana shigo da muggan makamai ta iyakokin Nijeriya.

Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Mungono
Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Mungono

Yayin da ya ke jawabi a wajen taron kaddamar da sabbin bindigogin jiragen ruwa biyu da hukumar kwastam ta yi a Lagos, Monguno ya ce ‘yan Nijeriya da dama sun mutu sakamakon muggan makaman da ake fasa-kwaurin su.

Ya ce gwamnatin tarayya ba za ta saduda a kan duk wata makarkashiya ko matsin lamba daga kowace kungiya ko mutane akan rufe iyakokin Nijeriya ba.

A cewar sa, wasu kasashe da ke makwaftaka da Nijeriya, sun mara wa gwamnatin tarayya baya a kan yadda za a tabbatar da tsaron iyakokin Nijeriya.

Karanta Wannan: Tsaro: Rundunar Yan Sanda Ta Ceto Mutane 22 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Imo

Munguno, ya ce shirin Operation Swift Response da ke gudana yanzu haka a iyakokin Nijeriya ya na samun nasara sosai, inda ya bada tabbacin cewa gwamnati ta jajirce domin tallafa wa duk hukumomin tsaro domin ba su damar yin maganin masu hannu a fasa-kwauri.