Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole, ya ce APC za ta yi wa PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar biji-biji a gaban Kotun Koli.
Jim kadan bayan kammala shari’ar sa da shugaba Muhammadu Buhari dai, Atiku Abubakar ya ce hukuncin cin fuska ne da rashin adalci, don haka zai garzaya zuwa Kotun Koli.
Yayin da Oshiomhole ya kammala ganawa da Shugaba Buhari a Abuja, ya ce jam’iyyar APC ta yi shirin sake kada jam’iyyar PDP da Atiku a Kotun Koli.
Ya ce matsawar da dokar Nijeriya za a yi hukunci, to ko Kotun Duniya Atiku da PDP za su je ba su damu ba, domin sun san bata lokaci kawai za su yi ba nasara za su samu ba.
Oshiomole ya kara da cewa, dokar Nijeriya ba ta PDP ko APC ba ce, hujjar da aka gabatar mata kawai za ta yi amfani da ita.
Ya
ce idan aka dubi yadda alkalan Kotun su ka yi biji-biji da hujjojin da PDP da
Atiku su ka gabatar, to ko wanda bai san shari’a ba ya san ba su da madogara, don
haka shugaba Buhari a shirye ya ke ya sake kafsawa da Atiku a gaban Kotun Koli.
You must log in to post a comment.