Home Labaru Kiwon Lafiya Tarin Fuka: Nijeriya Da Wasu Kasashe Na Cikin Hadarin Gaske – WHO

Tarin Fuka: Nijeriya Da Wasu Kasashe Na Cikin Hadarin Gaske – WHO

367
0

Sakamakon binciken Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO, ya nuna cewa Nijeriya da wasu kasashen Afrika bakwai ba su iya maida hankali wajen dakile yaduwar tarin fuka a kasashen su ba.

Kasashen kuwa sun hada da India da China da Indonesia da Philippines, da Pakistan, daNijeriya, da Bangladesh da Africa ta kudu.

Rahoton ya nuna cewa, cutar ta na kara yaduwa a wadannan kasashe, inda yanzu haka wasu mutane da su ka kai kashi 66 cikin 100 sun kamu da cutar a wadannan kasashe.

Nijeriya dai za ta iya dakile yaduwar cutar ne idan ta daina yawan dogaro da tallafin da ta ke samu daga kasashen waje, sannan ta shirya hanyoyin samar da isassun magunguna, da karin ma’aikata tare da horar da su yadda za su iya gano cutar da wuri.

Idan dai ba a manta ba, bincike ya nuna cewa, mutane miliyan 10 sun kamu da tarin fuka a duniya a shekara ta 2018.

Leave a Reply