Sa’o’i kadan bayan kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP, kudan zuma sun tarwatsa taron da aka fara a filin wasa na jihar Kogi da ke birnin Lokoja.
Magoya bayan dan takarar jam’iyyar PDP sun yi zargin akwai sa hannun wasu makiyan su, tare da jaddada cewa ko da wuta za a kona su su na nan a kan ra’ayin su.
Kudan Zuman dai sun harbi wasu daga cikin mahalarta taron, yayin da dama su ka sauya shawara sakamakon jin mummunan lamarin.
Duk da harin kudan zuman, wasu daga cikin magoya bayan Wada koma, tare da yin jerin-gwanon jiran isowar tauraron su.
Daga cikin mahalarta taron kuwa akwai Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus, da Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, da gwamnonin jihohin Benue da Taraba, da Bauchi da Sokoto.