Home Labaru Babbar Magana: Jami’an EFCC Sun Kama Ibrahim Magu Na Bogi

Babbar Magana: Jami’an EFCC Sun Kama Ibrahim Magu Na Bogi

530
0

Ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC na yankin Fatakwal, ya sanar da kama wani mutum da ake zargi da yin basaja da sunan shugaban hukumar Ibrahim Magu.

An dai kama mutumin ne ya na yi wa daraktocin hukumar habbaka ci-gaban yankin Neja Delta barazana.

Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa data fito daga hukumar.

Wanda ake zargin mai suna Robert Swem Terfa, ya bukaci cin hanci ne daga jami’an hukumar raya yankin Neja Delta domin Kashe zargin rashawa da ake yi masu.

An dai kama Terfa ne a Otal din Juanita da ke Fatakwal, inda ya ke taro da daraktocin hukumar bayan ya tallata masu hanyar da zai bi wajen cire sunayen su daga cikin jerin wadanda ake zargi a hukumar, inda ya shaida masu cewa yana wakiltar Magu ne.

Terfa, ya kara tabbatar masu cewa, za a cire sunayen su daga jerin sunayen da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada domin bincike a hukumar habbaka ci-gaban yankin Neja Delta.