Home Labaru Tarar MTN: Kamfanin Ya Biya Naira Biliyan A Kan Yin Rijista...

Tarar MTN: Kamfanin Ya Biya Naira Biliyan A Kan Yin Rijista Ba Bisa Ka’ida Ba

338
0

Kamfanin sadarwa na MTN ya biya tarar naira biliyan 235 daga cikin jimillar tarar naira biliyan 330 da hukumar sadarwa ta kasa NCC ta kakaba masa.

Mataimakin shugaban hukumar Farfesa Umar Dambatta ya bayyana haka a lokacin wata zantawa da ya yi da manema labarai a Abuja.

Dambatta ya kara da cewa, biyo bayan matsalar da kamfanin MTN ya samu, yanzu haka ya ba ‘yan Nijeriya damar sa hannun jari a kamfanin, bayan sa kamfanin da hukumar sadarwa ta kasa ta yi a cikin kasuwar hannun jari ta Nijeriya.

Umar Danbatta ya ce, daga cikin yarjejeniyar da aka cimma wa da kamfanin MTN na biyan tarar naira biliyan 330, yanzu haka sun biya naira biliyan 235.

Idan dai ba a manta ba, a watan Oktoban shekara ta 2015 ne hukumar sadarwa ta kasa NCC ta ci kamfanin MTN tarar naira tiriliyan 1 da biliyan 4 na yin rijistar layukan waya ba bisa ka’ida ba, sai dai bayan doguwar tattaunawa tsakanin kamfanin da gwamnatin tarayya, an rage tarar zuwa naira biliyan 330.

Leave a Reply