Home Labaru Tsaro: ‘Yan Sanda A Nasarawa Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 14...

Tsaro: ‘Yan Sanda A Nasarawa Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 14 A Jihar

1192
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta kama wasu miyagun mutane 14 da suka addabi al’umma a kan ayyukan ta’addancin garkuwa da mutane.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bola Longe ya sanar da haka a lokacin da ya ke gabatarwa manema labarai jerin ‘yan ta’addan a birnin Lafiya.

Bola Longe ya kara da cewa, rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar kama ‘yan ta’addan ne a wani simame da jami’an ta suka kai moboyar ‘yan ta’addan da ke Mararraban Udege a karamar hukumar Toto.

Da ya ke tabbatar wa al’ummar jihar kokarin rundunar na samar da tsaro a jihar, Bola Longe ya ce bincike zai ci-gaba da gudana a kan wadanda aka kama domin gurfanar da su gaban Kuliya.

Leave a Reply