Home Labaru Jam’iyyar APC Ta Yi Kira Ga Atiku Ya Kame Bakin Sa

Jam’iyyar APC Ta Yi Kira Ga Atiku Ya Kame Bakin Sa

481
0
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’yyar PDP
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’yyar PDP

Jam’iyyar APC ta gargadi tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya guji yi wa gwamnatin tarayya katsalandan a lamarin bai shafe shi ba.

Mai Magana da yawun jam’iyyar, Lanre Issa-Onilu ya bayyana haka a lokacin da yake cewa ya kamata Atiku ya bambance ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma tsoma baki cikin al’amuran da suka shafi tsaro, da dokokin kasashen waje da kuma alakar diflomasiyya.

Yace sun lura cewa Atiku, yana fitar da wasu sanarwa da suka shafi Sojin Najeriya, da tsaro da kuma alakar diflomasiyya domin nemna gurgunda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar APCn ta ce Atiku, ya sani tsayawar sa takarar shugaban kasa ba ta bashi kariyar fin karfin doka ba, don haka abin da yake fadi  babban laifi ne da cin amanar kasa.

Lanre Issa-Onilu, ya yi kira ga hukumomin tsaro su dauki mataki a kan Atiku, kamar yadda zasu dauka akan duk wani dan Najeriya da ya aikata irin wannan laifi, ba tare da la’akari da matsayin sa ba.