Home Labaru Tantance Ministoci: Majalisar Bata Sanar Da Buhari Komai Ba

Tantance Ministoci: Majalisar Bata Sanar Da Buhari Komai Ba

238
0

Fadar shugaban kasa ta ce har yanzu majalisun dokoki ba su sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari komai ba, game da tabbatar da sunayen ministoci 43 da ya aike musu.

Mai taimakawa shugaban kasa akan harkokin majalisar dattawa, Ita Enang, ya sanar da haka a Abuja, ya ce dole sai majalisun dokokin sun mika takarda ga bangaren shugaban kasa kafin a sa ranar rantsar da sabbin ministocin.

A ranar Talata daga gabata ne  majalisar dattawa ta tabbatar da zababbun ministocin guda 43, inda ake ganin cewar  za a rantsar da su,  a ranar Labara  daga gabata.