Home Labaru Rikicin Kabilanci: An Kulle Jami’ar Tarayya Da Ke Wukari A Jihar Taraba

Rikicin Kabilanci: An Kulle Jami’ar Tarayya Da Ke Wukari A Jihar Taraba

604
0

Shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke garin Wukari a jihar Taraba Farfesa Abubakar Kundiri, ya bada umarnin kulle cibiyar ilimin sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a garin Wukari tsakanin kabilun Tibi da Jukunawa.

Farfesa Kundiri ya bada umarnin dakatar da duk wasu al’amura a jami’ar ne, sakamakon garkuwa da wasu ‘yan bindiga su ka yi da wasu dalibai har ma da malaman makarantar.

Rajistiran jami’ar Magaji Gangumi ne ya sanar da kulle makarantar a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ya zama wajibi a kulle jami’ar saboda zanga-zangar da dalibai ke yi.

Ya ce an kulle jami’ar ne, biyo bayan zanga-zangar da dalibai su ka yi game da sace wasu abokan su da aka yi a kan hanyar Wukari zuwa Katsina-Ala a ranar Talatar da ta gabata, don haka ake umartar dalibai su fice daga dakunan kwanan su da ke cikin jami’ar.