Home Labaru Rundunar Sojin Najeriya Ta Kafa Bataliya A Daura

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kafa Bataliya A Daura

581
0

Rundunar sojojin Najeriya ta kafa  sabuwar Bataliya a garin Daura, dake jihar  Katsina.

Rundunar  ta ce an kafa Bataliya ta 171 a Daura, domin su rika sa ido akan mahara daga bangaren kan iyakan Arewacin ta Jihar Katsina, inda aka yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Karanta Wannan: Takaddama: An Bayyana Wa Kotun Zabe Cewa Shugaba Buhari Ya Yi Jarrabawar Waec

Ta ce cewa bataliyar za ta taya Rundunar Mayaka ta 17 ta Sojan Infantry da kuma Bataliya ta 35 dake Katsina, babban birnin jihar.

Rundunar za ta kasancewa a karkashin wasu ‘zaratan sojoji da aka kafa tun cikin watan Mayu 2017 a Daura kuma a karkashin Bataliya ta 35 ne aka kafa ta a 2017.

A yanzu Bataliyar Katsina ta 35 da wannan sabuwa ta 171 da aka kafa a Daura, duk za su kasance ne a karkashin shelkwatar Sojan Infantry dake Katsina.

Tun bayan da Buhari ya zama shugaban kasa matsalar tsaro ta kara tabarbarewa a Jihar Katsina da sauran jihohin dake makwabtaka da ita.

Tuni da aka bada umarnin cewa bataliyoyin sojojin dake fadin Najeriya  su yi karo-karon sojoji, a hada bataliya guda mai karfi ta zaratan sojojin da za a tura Daura dake jihar  Katsina.

.