Home Labarai Tambuwal Ya Maye Gurbin Gwamna Fayemi A Matsayin Shugaban Kungiyar Gwamoni

Tambuwal Ya Maye Gurbin Gwamna Fayemi A Matsayin Shugaban Kungiyar Gwamoni

34
0

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya maye gurbin takwaran sa na jihar Ekiti Kayode Fayemi a shugabancin kungiyar gwamnonin Nijeriya.

Tambuwal ya karbi shugabancin ne, a wajen taron majalisar tattalin arziki ta kasa da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda gwamna Fayemi ya mika ma shi ragamar shugabancin.

Wata Sanarwar da daraktan yada labarai na na kungiyar gwamnonin Abdulrazaq Bello Barkindo ya fitar, ta ce Tambuwal ya yi aiki tukuru cikin gaskiya da aminci lokacin da ya ke mataimakin shugaban kungiyar a karkashin shugabancin Fayemi tsawon na shekaru hudu.

Sanarwar, ta ce Tambuwal zai rike mukamin ne har zuwa watan Mayu na shekara ta 2023, lokacin da za a sake gudanar da sahihin zabe na kungiyar.