Home Labarai ‘Yan Sanda Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Masu Tarin Yawa A Jihar Katsina

‘Yan Sanda Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Masu Tarin Yawa A Jihar Katsina

46
0

‘Yan ta’adda da dama ne su ka sheka barzahu a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, yayin da tawagar ‘yan sanda su ka afka masu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an samo bindiga kirar AK47 guda daya, da motocin ‘yan ta’addan hudu da aka samu a wurin da aka yiartabun.

Kamar yadda wani rahoton ‘yan sanda ya bayyana, sama da ‘yan ta’adda 30 a kan babura dauke da manyan bindigogi, sun rufe hanyar Sabuwa zuwa Mararrabar Yakawada domin shirin yin fashi da garkuwa da mutane, kafin ‘yan sanda sun bankado magun shirin.

Bayan samun kiran gaugawa, DPO na karamar hukumar Sabuwa ya ce sun gaggauta kama hanya, inda ya jagoranci jami’an tsaro su ka afka wa ‘yan ta’addan tare da samun nasarar fatattakar su.

Da yawa daga cikin ‘yan ta’addan an kashe su, yayin da wasu su ka tsere da raunika, don haka ana ciigaba da binciken lamarin kamar yadda SP Gambo Isah ya bayyana.