Home Labarai Ummita: Majalisa Ta Bukaci a Binciki Zargin Kisan Da Dan China Ya...

Ummita: Majalisa Ta Bukaci a Binciki Zargin Kisan Da Dan China Ya Yi A Kano

47
0

Majalisar Wakilai ta bukaci shugaban rundunar ‘yan Sandan Nijeriya ya binciki zargin da ake yi wa dan kasar Chinan Geng Quanrong na kashe budurwar sa Ummulkulthum Buhari a jihar Kano, biyo bayan amincewa da kudurin da dan majalisa Kabiru Alhasan Rurum ya gabatar a gaban majalisar.

Da ya ke gabatar da kudurin, Rurum ya ce an aikata kisan ne a gidan marigayiya da ke unguwar Janbulo a birnin Kano, ya na mai cewa Ummita ta gamu da ajalin ta ne a daidai lokacin da ta ke yi wa kasa hidima a jihar Sokoto.

Ya ce sun damu matuka kasancewar kwana biyar bayan aikata laifin, har yanzu ‘yan sanda sun ki su fito da cikakkun bayanan binciken su a kan kisan.

Rurum ya kara da cewa, kare rayuka da mutuncin ‘yan kasa shi ne babban aikin gwamnati, hakan ya sa ya zama wajibi su dauki lamarin da muhimmanci, sdomin iyalan marigayiyar da sauran
‘yan jihar Kano da ma Nijeriya baki daya su na son a yi aiki da doka.

A karshe Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya ba da umarnin a yi shiru na tsawon minti daya domin tunawa da marigayiya Ummita.