Home Labaru Tallafi: Shugaba Buhari Ya Jinjina Wa Bill Gates Da Dangote

Tallafi: Shugaba Buhari Ya Jinjina Wa Bill Gates Da Dangote

552
0
: Shugaba Buhari Ya Jinjina Wa Bill Gates Da Dangote
: Shugaba Buhari Ya Jinjina Wa Bill Gates Da Dangote

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jinjina wa gidauniyar Bill da Melinda Gates da gidauniyar Aliko Dangote, bisa taimako da ayyukan ci-gaban da su ke gudanarwa a Nijeriya.

Karanta Wannan: Tattalin Arziki: Najeriya Na Maraba Da Masu Zuba Jari – Buhari

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa a kan shafukan yanar gizo Bashir Ahmad ya fitar a Abuja, ya ce Buhari ya yi jinjinar ne a wata ganawa da ya yi da attajiran biyu a gefen taron majalisar dinkin duniya a birnin New York na kasar Amurka.

Shugaba Buhari, ya ce mutanen biyu sun taba rayukan mutane da dama ta bangaren ciigaba, sannan ya taya su murna a kan cimma abubuwan da su ka shirya yi.

Aliko Dangote dai ya bayyana fatan wata rana ya rika sadaukar da dukiyar sa tamkar hamshakin mai kudin duniya Bill Gates.