Home Labaru Ilimi Jarabawar JAMB: Sai Da Shaidar Yin Rajistar Katin Zama Dan Kasa –...

Jarabawar JAMB: Sai Da Shaidar Yin Rajistar Katin Zama Dan Kasa – Hukuma

403
0
Jarabawar Jamb: Sai Da Shaidar Yin Rajistar Katin Zama Dan Kasa - Hukuma
Jarabawar Jamb: Sai Da Shaidar Yin Rajistar Katin Zama Dan Kasa - Hukuma

Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’o’i JAMB, ta ce daga yanzu rubuta jarabawar sai dalibi ya mallaki katin zama dan kasa ko kuma lambar rajistar mallakar katin da hukuma ke badawa.

Kakakin hukumar Fabian Benjamin ya bayyana wa manema labarai haka a Legas, inda ya ce tuni har hukumar ta fara saida fom na jarabawar shekara ta 2020.

Benjamin, ya ce hukumar JAMB ta shirya tsarin ne domin toshe kafafen da dalibai ke bi su na satar jarabawa.

Don haka ya yi kira ga daliban su tabbatar sun yi rajista da hukumar bada katin zama dan kasa domin samun lamba, saboda rashin ta zai sa a hana mutum rubuta jarabawar.

Ya ce daga yanzu za a rika yin rajistar jarabawar JAMB ne a wuraren da hukumar bada katin zama dan kasa ta bude ko kuma ta amince da su a fadin Nijeriya.