Home Labaru Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Murabus

Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Murabus

201
0
Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Murabus
Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Murabus

Jam’iyyar PDP ta maida martani a kan maganar da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi, inda ya ce zai jingine kariyar da gwamnati ta ke ba shi domin a bincike shi a kan zargin da ake yi ma shi.

Mai auke da sa hannun Kakakin ta na kasa Kola Ologbondiyan
Mai auke da sa hannun Kakakin ta na kasa Kola Ologbondiyan

A cikin wata sanarwa jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun Kakakin ta na kasa Kola Ologbondiyan, ta kalubalanci Osinbajo da cewa idan ya isa ya aikata abin da ya furta.

Jam’iyyar PDP, ta bukaci Osinbajo ya jingine kariyar da gwamnati ta ke ba shi kamar yadda ya fada, sannan ya yi murabus daga kujerar sa a bincike shi a kan zargin da ake yi ma shi na cin hanci.

Karanta Wannan: PDP Ta Zargi Jonathan Da Matar Sa Da Yi Wa Jam’iyyar APC Aiki

A karshe PDP ta bukaci mataimakin shugaban kasar yay a yi murabus domin ya fuskanci bincike, domin babu yadda za a bincike shi alhalin ya na da mukamin mataimakin shugaban kasa.