Home Labaru Tallafi: Gwamnatin Katsina Za Ta Kirkiro Hukumar Jin Ra’ayin Jama’a

Tallafi: Gwamnatin Katsina Za Ta Kirkiro Hukumar Jin Ra’ayin Jama’a

174
0
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina na shirin kafa wata hukuma da za ta kula da bukatun mutane masu bukata ta musamman a jihar.

Mai taimakawa gwamna na musamman akan lamurran mutane masu bukata ta musamman Ya’u Rufa’i Zakka, ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga mutane masu bukata ta musamman da suka fito daga yankunan kananan hukumomi 11.

Ya’u Zakka, ya ce gwamnati mai ci yanzun ta na sane da kokarin da mutane masu bukata ta musamman suka yi a lokacin zabe.

Ya bayyana cewa batutuwan da suka shafi bunkasa rayuwar mutane masu bukata ta musamman za su samu kyakkyawar kulawa daga gwamnati.

A jawabin shugaban makarantar kurame ta gwamnati dake Malumfashi Malam Halliru Dogo, ya godewa mai taimakama gwamnan na musamman akan ziyarar wanda ya bayyana a matsayin irinta ta farko.