Home Labaru Kasafin 2021: Katsina Za Ta Ciwo Bashin Naira Biliyan 50 Domin Kammala...

Kasafin 2021: Katsina Za Ta Ciwo Bashin Naira Biliyan 50 Domin Kammala Manyan Ayyuka

138
0

Gwamnatin Jihar Katsina, za ta ciwo bashin naira miliyan dubu hamsin domin kammala manyan ayyukan da ta faro.

Kwamishinan kasafin kudi da tattalin arziki na Jihar katsina, Faruk Jobe, ne ya bayyana wa manema labarai haka, a gidan gwamnati jihar Katsina, bayan kammala zaman majalisar zartaswa karo na shidda, da gwamna Aminu Bello Masari ya jagoranta.

Faruk Jobe, ya kara da cewa akwai abubuwan da aka yi la’akari da su, na wasu manyan ayyukan da wannan gwamnati ta faro, wanda ya zama wajibi a kammala su.

Ya ci gaba da cewa shi ya sa suka shirya wani shirin ko ta kwana, na shirya yarjejeniya da wasu kamfanoni masu zaman kan su, da za su samar da wasu kudade a matsayin ba shi, domin kammala ayyukan da suka faro.