Babban bankin duniya ya ware dalar amurka miliyan biyar kwatankwacin naira biliyan daya da miliyan dari takwas domin gudanar da wasu muhimman ayyuka a jihar Katsina.
Bankin zai gudanar da aikin magance matsalar zaizayar kasa tare da aikin magance matsalar ambaliyan ruwa a jihar ne Katsina, kamar yadda shugaban aikin Amos Abu ya bayyana.
Dakta Amos ya kara da cewa, yanzu haka ana gudanar da irin wadannan ayyuka a jihohi 20 na Nijeriya, amma jihar Katsina za ta samu kulawa na musamman sakamakon yadda matsalolin su ka yi mata katutu.
Ya ce tsarin gudanar da aikin shine, kowacce jiha zata samar da wani kaso na kudaden daga aljihun ta, sai bankin ya basu karin tallafin kudade da za a kammla aikin da su.
A nashi jawabin, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce, akalla mutane 3,000 ne suka mika kokon barar su ga gwamnatin jihar don neman ta magance musu matsalolin zaizayar kasa da ta ambaliyar ruwa.
Sai dai gwamnan ya ce, jihar Katsina ta kashe makudan kudade da yawan su suka kai naira biliyan shida wajen shawo kan wadannan matsaloli.
You must log in to post a comment.