Hukumar binciken hatsari ta kasa AIB ta fitar da rahotannin a kan wasu binciken hatsarin jiragen sama hudu tare da bada shawarwari 24.
Daga cikin rahotannin da hukumar ta fitar, akwai na hatsarin da ya rutsa tsohon gwamnan jihar Taraba, Danbaba Sunati, wanda ya fadi a daf da filin jiragen sama na Yola a ranar 25 ga watan Oktoba na shekara ta 2012.
Da ya ke jawabi a kan rahotannin binciken, kwamishina hukumar Akin Olateru ya ce binciken da suka gudanar a kan hatsarin tsohon gwamnan ya nuna cewa, marigayin bashi da kware na tuka jirgi.
Idan dai ba a manta ba, Dan-baba Suntai ya tsira a hatsarin jirgin, inda daga bisani aka ci-gaba kula da lafiyar sa a asibiti domin ganin ya samu lafiya, amma a karshe ya mutu a shekara ta 2017.
A cewar shugaban hukumar, tsohon gwamnan na da direban sa mai cikakken lasisi tuka jirgi, amma ya zabi ya rika tuka da kan sa duk da cewa bai samu takardar amincewa daga hukumar kula da jiragen sama ta kasa ba.
A karshe Olateru ya yi kira ga hukumar kula da jiragen sama ta kasa NCAA ta kara mayda hankalin a aikinta na kula da duk wani jirgi da ke tashi zuwa sararin samaniyar Nijeriya.