Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya umarci ‘yan sandan kasar’nan su rika yin aikin sa’o’i takwas a kowace rana, don rage musu damuwar da ke sa su na kashe mutane a cikin ganganci.
Muhammad Adamu ya bada umarnin ne a hedkwatar ‘yan sanda da ke Abuja, a yayin wani taro da ya yi da shugabannin ‘yan sandan a kan fannin lafiya na hukumar.
An bude fannin lafiya na hukumar ‘yan sandan ne a shekara ta 1975, domin samar wa jami’an ‘yan sanda masu aiki da wadanda suka kammala aiki magunguna kyauta.
Yayin da ya ke jawabi Adamu ya ce, ya bada umarnin rage lokacin aikin ‘yan sandan ne, bayan sun yi la’akari da irin yadda jami’an ke daukar sa’o’i masu yawan suna gudanar aiki, wadda hakan ke haddasa musu gajiya matuka.
You must log in to post a comment.