Home Labaru Talauci Ya Shafi Kowa A Nijeriya – Atiku

Talauci Ya Shafi Kowa A Nijeriya – Atiku

297
0
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa , Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa , Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ce idan ba a yi hankali ba, baki daya ‘yan Nijeriya za su fada cikin talauci.

Yayin da ya ke bayyana ra’ayin sa a kan rahoton hukumar shirin ci-gaba na majalisar dinkin duniya UNDP, wanda ke nuna cewa ‘yan Nijeriya miliyan 98 sun kasance a cikin talauci, Atiku ya ce hatta Aliko Dangote mai arzikin Afirka sai da talaucin da ke ci-gaba da yaduwa a Nijeriya ya taba shi.

Karanta Labaru Masu Alaka: An Yi Jayayya Tsakanin Bangaren Buhari Da Atiku A Kotu

Atiku Abubakar, ya zargi wadanda su ka sa Nijeriya cikin wannan halin a matsayin marasa kishi, inda ya ce barazana a kan tsaron da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu ba lamarin Boko Haram ko ‘yan bindiga ba ne, illa kasancewar kasar ta tsunduma cikin tarin talauci a tarihi.

Haka kuma, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su hada hannu don neman mafita a kan lamarin, ya na mai cewa gazawar tattalin arzikin Nijeriya a cikin shekaru hudun da su ka gabata ya shafi kowa daga sama har kasa.