Home Labaru Siyasa CBN Ya Bada Lasisin Sabon Bankin Musulunci A Nijeriya

CBN Ya Bada Lasisin Sabon Bankin Musulunci A Nijeriya

229
0
Babban bankin Nijeriya
Babban bankin Nijeriya

Rahotanni sun nuna cewa, babban bankin Nijeriya, CBN ya bada lasisin fara aikin wani sabon bankin Musulunci a Nijeriya, mai suna TAJ Bank Limited.

Karanta Wannan: Shigo Da Manja: Buhari Ya Umurci CBN Ya Dau Mataki Akan Kamfanoni

CBN ya sanar da fara aikin sabon bankin ne a cikin wata wasika da ya aika wa bakin a ranar Litinin din da ta gabata, sakamakon gamsuwa da sharuddan da ya gindayawa bankin.

Sai dai bankin CBN ya iyakance cewa, aikin bankin zai tsaya ne a yankunan Arewa maso yamma da Arewa maso gabas, amma an bashi damar samar da babban ofishin sa a Abuja.

Ci-gaba da aka samu dai, ya kawo adadin bankunan Musulunci a Nijeriya biyu, bayan samun bankin Musulunci na Jaiz a shekara ta 2011.

Idan dai za a iya tunawa, a shekara ta 2003 aka kaddamar da Jaiz a matsayin cibiyar hada-hada cinikayyar Musulunci da babu riba a ciki, yayin da a shekara ta 2011 bankin CBN ya bankin lasisin fara aiki a yankin Arewacin Nijeriya, don haka ya zama bankin Musulunci na farko a Najeriya.