Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Dakushe Nasarorin Buhari – Soyinka

‘Yan Bindiga Sun Dakushe Nasarorin Buhari – Soyinka

208
0
Farfesa Wole Soyinka, Fitaccen Marubuci
Farfesa Wole Soyinka, Fitaccen Marubuci

Fitaccen marubuci Farfesa Wole Soyinka, ya ce matsalolin tsaron da ke addabar ‘yan Nijeriya musamman hare-haren ‘yan bindiga, sun dakushe nasarorin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu.

Soyinka ya bayyana haka ne, yayin da yak e kokawa da karuwar hare-haren ‘yan bindiga da ake dangantawa da makiyaya a sassan Nijeriya.

Yayin da ya ke tsokaci a kan halin da tsaro ke ciki a Nijeriya, Soyinka ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da gazawa wajen daukar matakan da su ka dace don kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga, lamarin da ya ce ya yi sanadin salwantar rayukan ‘yan Nijeriya da dama.

Karanta Labaru Masu Alaka: Samar Da Rugage Zai Haifar Da Matsala A Nijeriya – Inji Wole Soyinka

Farfesan ya kara da cewa, sha’anin tafiyar da mulkin Nijeriya ya na da matukar wahala, duba da tarihin kafuwar ta da ginshikan da su ka kafa ta, da siyasa da kuma al’adu.

Marubucin, ya kuma zargi ‘yan siyasar Nijeriya da fifita neman kudi ta kowane hali fiye da bukatun talakawa, matsalar da ya ce ta haifar masu da dimuwa da rashin fahimtar nauyin da ya rataya a wuyan su.