Home Labaru Take Hakki: An Fara Shari’ar Omar Al-Bashir Na Sudan

Take Hakki: An Fara Shari’ar Omar Al-Bashir Na Sudan

359
0

A dai dai lokacin da ya fara fuskantar shara’a tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir, ya amince da karbar tsabar kudi har Dala miliyan 90 daga masarautar Saudiya.

Wani jami’in bincike mai mukamin Birgediya a rundunar ‘yan sandan kasar, Ahmed Ali, ya shaida wa kotun birnin Khartoum cewa, tsohon shugaban ya fada masa, ayarin yarima mai jiran gadon mulkin Saudiya, Muhammad bin Salman, ne ya kawo masa makuden kudaden.

A wannan Litinin ne dai Omar Al-Bashir, wanda ya mulki Sudan tsawon shekaru 30 ya isa kotun, inda ake yi masa shari’a cikin tsattstsauran tsaron jami’an sojoji.

An jiyo dangin sa na daga murya suna kabbara (Allahu Akbar), yayinda shi ma ya yi makamanciyar kabbarar.

Tsohon shugaban Sudan na fuskatar tarin tuhuma ne kan aikata laifukan yaki, da cin zarafin al’umma, da kisan kare dangi daga Kotun Hukunta masu aikata manyan Laifuka ta Duniya.

A ranar 11 ga watan Afrilun da ya gabata ne dai aka tilasta wa Al-bashir, sauka daga madafun iko bayan ‘yan kasar sun kwashe watanni suna zanga-zanga.
am”�4��o8

Leave a Reply