Home Labaru Zanga-Zangar Hong Kong: China Ta Gargadi Kanada

Zanga-Zangar Hong Kong: China Ta Gargadi Kanada

169
0

Ofishin jakadancin kasar Sin wato China a Kanada ya gargadi kasar ta kiyayi sanya baki a harkokin cikin gidan yankin Hong Kong, kwana guda bayan China ta kare kanta daga zargin take hakki.

Gabanin kare kan daga gwamnatin China, an ji ministar harkokin kasashen wajen kasar Kanada Chyrstia Freeland, da shugabar manufofin harkokin wajen kungiyar EU Federica Mogherini, suna jaddada muhimmancin ‘yancin fadin albarkarcin baki da kuma zanga-zangar lumana a matsayin wajibi bayan sun bayyana takaici game da yadda rikici ke kara kamari a Hong Kong.

Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin cigaba da kyamar gwamnatin yankin har ta amince da bukatun su, duk kuwa da irin kiraye-kirayen sulhun da kasashe ke yi wa bangarorin biyu.