Home Labaru Binciken Obasanjo: Kungiyar SERAP Ta Ce Tana Goyon Baya

Binciken Obasanjo: Kungiyar SERAP Ta Ce Tana Goyon Baya

370
0

Kungiyar tabbatar da adalci da kuma shugabanci na gari wato SERAP, ta ce ta na goyon hukumar EFCC a kan binciken da za ta yi wa tsohon shugaban  kasa Olusegun Obasanjo, kan kudin Lantarki naira billiyan 16.

Kungiyar ta ce wannan wata dama ce da hukumar yaki da rashawa za ta yi amfani da shi  na  kawar da zargin cewar ba a binciken  masu manyan matsayi a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar Kolawale Oluwadare, ya fitar, ta ce binciken ya zo kan gaba musamman a lokacin da al’ummar Najeriya suka matsu wajen ganin ana binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma take hakkin dan adam.

 Kungiyar ta ce binciken wani abu ne da ta dade ta son ganin ana gudanar wa, musamman akan yadda ‘yan Najeriya suka zaku suke son ganin an gudanar da bincike a bangaren, saboda matsalar da suke fuskanta na rashin wutar lantarki, duk da cewar suna biyan kudin wuta.