Home Home Takarar Musulmi Da Musulmi:  Babachir Ya Ce APC Ba Za Ta Ci...

Takarar Musulmi Da Musulmi:  Babachir Ya Ce APC Ba Za Ta Ci Zaben Shugaban Kasa Ba

32
0

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma jigo a jam’iyyar APC, Babachir Lawan ya ce, jam’iyyar ba za  ta ci zaben shugaban kasa da za a yi a 2023 ba saboda zaben mataimaki Musulmi da dan takarar shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ya yi.

A tattaunawar sa da BBC Mista Babachir ya ce, sun yi bakin kokarin su domin ganin Tinubu wanda shi ma Musulmi ne, ya samu takara, amma daga baya sai suka fahimci ya yi musu rufa-rufa game da abokin takara ko mataimakin sa, lamarin da ya sa suka juya masa baya.

Tsohon sakataren ya ce APC ba za ta kai labari ba a zaben shugaban kasa, kuma zai iya faden jihohin da Bola Tinubu zai iya cin zabe da kuma wadanda ba zai ci ba, kuma shi ba ya Bola Tinubu yanzun dan baya goyon bayan tkitin Musulmi da musulmi.

Babachir ya kara da cewa PDP sun zo sun tattauna da su, kuma sun yarda za su yi musu abin da suke soi dan suka hada kai saboda haka sun yarda za su yi musu aiki.

Ya ce su ma ‘yan jam’iyyar Labour kusan kwana suke yi  a wajen su domin su tafi tare da su.