Home Home Gargadi: Obasanjo Ya Ce  Yara Miliyan 20 Da Basa Zuwa Makaranta Ka Iya...

Gargadi: Obasanjo Ya Ce  Yara Miliyan 20 Da Basa Zuwa Makaranta Ka Iya Zama ‘Yan Boko Haram

33
0

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa wajibi ne gwamnati ta dauki matakan gaggawa wajen magance matsalar tarin kananan yaran da ake da su wadanda basu zuwa makaranta ko kuma a fuskani karuwar mayakan Boko Haram miliyan 20.

A jawabin sa gaban taron kasa kan sauya fasalin tsarin ilimi mai zurfi da majalisar wakilai ta shirya, Obasanjo ya ce matukar ba a dauki matakan da suka dace wajen mayar da yara miliyan 20 makaranta ba ko shakka babu akwai hadarin su iya tsunduma cikin kungiyar Boko Haram.

Taron wanda ya gudana a Abuja ya mayar da hankali ne kan kalubalen da yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriyar ASUU ke haifarwa ga rayuwa ko kuma makomar dalibai.   

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yaran da basa zuwa makaranta babu ta hanyar da za su iya taimakawa wajen gina kasa, dalilin da ke nuna bukatar da ake da ita wajen tilastawa yara karatu don ci gaban kasar.

A cewar Obasanjo akwai bukatar tilasta zuwa makarantun Firamare da Sakandire ga dukkanin yaran Najeriya, yana mai cewa gwamnati ta gaza wajen iya rage yawan yaran da basa zuwa makaranta musamman a arewacin Najeriya da ake fama da matsalar ta’addanci.

Cikin yara miliyan 244 da basa zuwa makaranta a sassan Duniya, Najeriya ke da adadin yara miliyan 20 da ke matsayin kashi 10 na jumullar yaran marasa zuwa makaranta.