Home Home Rajistar Zabe: INEC Ta Ce Ba Zai Yiwu a Ci Gaba Ba

Rajistar Zabe: INEC Ta Ce Ba Zai Yiwu a Ci Gaba Ba

50
0

Hukumar zaɓe mai zaman Kanta ta Najeriya INEC ta ce dokokin Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ba su ba ta damar ta ci gaba da yin aikin rajistar kaɗa ƙuri’a ba kafin babban zaɓe na 2023.

A ranar Talata ne rahotanni suka ce babbar kotun tarayya a Abuja ta umarci hukumar ta ci gaba da aikin rajistar har zuwa saura kwana 90 kafin zaɓen.

Amma da yake magana ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels a ranar Talatar, Kwamashinan Wayar da Kan Masu Zaɓe na INEC Festus Okoye ya ce hukumar ba ta samu kwafin hukuncin ba tukunna.

Ya ƙara da cewa Abu ne da ba zai yiwu ba a tsarin Kundin Tsarin Mulki ga INEC ta ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe.

INEC dai ta rufe aikin rajistar zaɓen ne a watan Yuli da ya gabata, abin da ya jawo martani da koke-koke daga ƙungiyoyin farar hula cewa za a tauye wa miliyoyin ‘yan ƙasa haƙƙin su.