Gamayyar ‘yan Majalisar Wakilai daga jam’iyyu takwas, sun
amince su kiyaye da bin tsarin karɓa-karɓa da jam’iyyar APC
ta shigo da shi a shugabancin majalisar.
‘Yan Majalisar dai Sun amince da sharuɗɗan karɓa-karɓar ne, yayin da su ke ƙaddamar da gangamin yin ‘Maja’ a Abuja.
Zababbun ‘yan majalisar da su ka yi Majar dai sun hada na jam’iyyun APC da PDP da Labour da NNPP da APGA da SDP da ADC da YPP, sai dai ba dukkan ‘yan majalisar ba ne su ka amince da shiga Majar.
Da ya ke magana yayinn ƙaddamar da majar, dan majalisar na jam’iyyar APC Bello Kumo, ya ce har yanzu gamayyar ‘yan majalisar ba su da ɗan takarar da su ke goyon baya, amma su na jiran su ga tsarin karɓa-karɓar da za ta fitar.














































